1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hawan Arfa ya gudana a yanayi na tsananin zafi

Abdul-raheem Hassan MAB
June 27, 2023

Wasu Musulmi sun gudanar da kololuwar aikin Hajji da ke zama hawan Arfa. Wannan shi ne karon farko da aka samu maniyata masu yawa a tarihi tun bayan soke dokokin Corona. Sai dai sun yi fama dayanayi na tsananin zafi.

https://p.dw.com/p/4T7py
Alhazai sun yi addu’o'i Arfa a yayin gudanar da aikin hajjin bana a wajen birnin Makkah Hoto: Mohamed Abd El Ghany/REUTERS

Maniyata aikin Hajji sun gudanar da hawan Arfa a Jabal ar-Raḥmah, tsauni mai tsawon mitoci akalla 70, wanda ke da tazarar kilimita 20 da Kudu maso gabashin birnin Makka. Tarihi ya tabbatar da cewa a wurin ne Annabi Muhammad (SAW) ya gudanar da hudubar karshe. Hawan Arfa, shi ne kololuwar aikin hajji ga mahajjata da suka kwashe tsawon yini suna ibada da addu'o'i game da karatun Kur'ani har zuwa faduwar rana, daga nan suka wuce Muzdalifah.


A yanayi na tsananin zafi da ya kai maki 48 a ma'aunin celcius ne aka gudanar da ibadar. Wannan ya sa hukumomin kiwon lafiya na Saudiyya shawartar mahajjata amfani da lema don kare lafiyarsu, bayan jikkatar akalla alhazai 40 saboda tsananin zafi.

Saudi Arabien Hadsch Islam Pilgerfahrt
An ta fesa wa alhazai ruwa a yayin zuwa dutsen Arfa a aikin Hajjin bana a Saudiyya.Hoto: Amr Nabil/AP/picture alliance

Adadi mafi yawa na masu aikin Hajji

Alkaluman hukumar kula da alhazai ta Saudiyya na cewa wannan shi ne karon farko da aka samu yawan mahajjata a tarihi na kusan mutane miliyan biyu da rabi. Sai dai irin wanna cunkoson jama'a ya yi ta yin sanadiyyar rayukan alhazai ciki har da mutuwar mutane akalla 717 a shekarar 2015 a wani turmutsitsi, wanda shi ne karon farko da aka taba samu irin hatsarin cikin shekaru 25. Hajiya Ini Gangare daga jihar Plateau a Najeriya, ta ce a wannan karon an yi tsari da ya takaita hatsarin mutuwar mutane a cunkoso.

Arfa: ranar farin ciki ga sabbin maniyata

Saudi-Arabien, Mekka | BG Haddsch
Kamal Kabashi da Ahmed Jaber na Sudan na cikin mahajjatan banaHoto: Sajjad Hussain/AFP/Getty Images

Akalla shekaru uku a jere ne annobar Corona ta takaita adadin zuwan Musulmi aikin Hajji, in ban da wasu kalilan mazauna kasar Saudiyya da ke samun dama a cikin dokokin ba da tazara . Daga bisani ne aka kara yawan zuwa mutane 60 kacal daga kasar. Dya daga cikin Musulmi da suka samu daman sazke farali a bana na cewa: ""Ba zan iya kwatanta yadda nake ji ba, hawaye na fita daga idanuna. Kalamai sun yi kadan na iya kwatanta yadda nake ji. Babu wani abu da ya kai min wannan rana."

Musulmi na gudanar da aikin hajjin ne cikin matakan tsaro, inda hukumomin Saudiyya suka baza dubban jami'an tsaro a kusan dukkannin wuraren ibadu ciki har da jirage marasa matuka da ke sa ido kan motsin jama'a. Ana sa ran karkare aikin hajjin a anar Jumaa'a (29.06.2023).