1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shugaban gwamnatin Scotland ya yi murabus

April 29, 2024

Shugaban gwamnatin Scotland Humza Yousaf ya ajiye aiki gabanin kuri'ar yankar kauna da majalisa ke shirin kada masa kan matakin da ya dauka na raba gari da wasu kananan jam'iyyun kawance kan manufofin sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/4fJ4e
Shugaban gwamnatin Scotand mai murabus Humza Yousaf
Shugaban gwamnatin Scotand mai murabus Humza Yousaf Hoto: Jeff J Mitchell/Getty Images

Yousaf na fuskantar matsin lamba na yin murabus tun lokacin da jam'iyyarsa ta SNP ta yanke kawance da jam'iyyar Scottish Greens mai rahin kare muhalli a makon da ya gabata.

Karin bayani: Scotland za ta koma cikin kungiyar EU 

'Yan adawa daga jam'iyyar Scottish Conservative sun sha alwashin kada kuri'ar yankar kauna kan ministan a ranar laraba, kafin ya yi murabus a wannan rana domin kauce wa mummunar hamayya daga mambobin majalisar.

Karin bayani: 'Yankin Scotland na neman ballewa daga Birtaniya 

Yousaf shi ne musulmi na farko da ya jagoranci wata babbar jam'iyya a Burtaniya, wanda kafin zabarsa ya ke cike da fatan zai yi nasara.

Karin bayani: Scotland za ta ci gaba da zama a Birtaniya 

Majalisar dokokin Scotland wadda aka sake kafa ta a 1999, na da takaitaccen ikon yin dokoki da suka shafi lafiya da ilmi da sufuri da kuma muhalli, yayin da gwamnatin Burtaniya a birnin Landan ke da karfin tasiri kan al'amuran da suka shafi kasa baki daya kamar tsaro da manufofin kasashen waje.